Gwamnatin Kano ta ce za ta hada hannu da gwamnatin tarayya domin bunƙasa kiwon dabbobi da gina mayanka irin ta zamani da nufin samar nama mai tsafta wanda ba zai cutar da al’umma ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan lokacin ya karɓi baƙuncin Ministan bunkasa Kiwon Dabbobi na Najeriya, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, a fadar gwamnatin Kano.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Murtala Sule Garo, ya ce ganawar, bangarorin biyu ta mayar da hankali ne wajen tattaunawa akan hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jihar Kano da Gwamnatin Tarayya domin bunƙasa harkar kiwon dabbobi, inganta wadatar abinci, samar da ayyukan yi da kuma cin gajiyar dimbin damar tattalin arziki da ke cikin fanni.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta yi aiki tare da masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu domin samar da mayanka na zamani a Kano, wanda zai inganta sarrafa nama, ƙarfafa harkokin kiwo da samar da ƙarin guraben aikin yi ga al’ummar jihar.
Da yake jawabi, Ministan harkokin bunkasa kiwon dabbobi na Najeriya Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya ce, ya zo Kano ne domin faɗaɗa ayyukan hukumar sa da hada hannu da gwamnatin Kano la’akari da baiwar fannin kiwon da jihar take da shi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Garo na cewa jihar Kano za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da noma a Najeriya, don haka gwamnatin jihar ta himmatu wajen tallafawa duk wani shiri da zai zamanantar da fannin kiwon dabbobi da inganta rayuwar al’umma.
