Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin jihar Katsina ta haramta amfani da babura da daddare a fadin...

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta amfani da babura da daddare a fadin kananan hukumomi 19 na jihar a wani mataki na inganta tsaro

Date:

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta amfani da babura da daddare a fadin kananan hukumomi 19 na jihar a wani mataki na inganta tsaro.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Nasiru Mu’azu, ya fitar, ya ce an sanya dokar ne daga karfe 8 na dare. zuwa 6 na safe.
Umarnin ya shafi Kananan Hukumomin da ‘Yan fashi da masu aikata sauran laifuffuka suka addaba.
Kananan Hukumomin sun hada da Sabuwa,Dandume, Funtua, Faskari da Bakori sai Kankara, Danja, Kafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Danmusa, Safana ,Dutsinma.Haka zalika akwai Kurfi, Charanchi, Jibia, Batsari da kuma Kankia.
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su fahimci cewa manufar wannan umarnin shi ne maido da zaman lafiya na dindindin a yankunan da abin ya shafa.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...