Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar likitoci da likitocin hakora a kasar nan ta ce za ta...

Kungiyar likitoci da likitocin hakora a kasar nan ta ce za ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa a wata mai zuwa domin yanke shawara kan ko za ta shiga yajin aiki a fadin kasar

Date:

Kungiyar likitoci da likitocin hakora a kasar nan ta ce za ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa a wata mai zuwa domin yanke shawara kan ko za ta shiga yajin aiki a fadin kasar.
Shugaban kungiyar, Dr Victor Makanjuola ne ya bayyana haka a jiya Lahadi.
A cikin sanarwar kungiyar ta bayar da wa’adin kwanaki 21 ga gwamnatin tarayya ta biya bukatun ta ko kuma ta fuskanci yajin aiki biyo bayan taron da majalisar zartarwar kungiyar da ta gudanar a ranar 7 ga Agustan da muke ciki wanda kuma wa’adin yake karewa a yau Litinin.
Dokta Makanjuola y ace amma kungiyar ta ba gwamnati har zuwa ranar 31 ga Agustan nan, ta biya bukatun na ta.
Ya kara da cewa za su gudanar da taro daga ranar 4 ga wata 10 ga watan satumba mai kamawa wanda a nan ne kuma za su tsaida matsaya kan tafiya yajin aikin in har gwamnati ba ta yi wani abu ba har zuwa lokacin.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...