Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, a matsayin Amirul Hajjn jihar na shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Fadar Sarkin Rano, bayan halartar bikin naɗin rawani na Muhammad Abubakar Isa, babban ɗan Sarkin Rano.
Gwamna Yusuf ya ce an zaɓi Sarkin Rano domin jagorantar tawagar alhazan jihar ne bisa tsarin baiwa masarautun jihar damar jagorantar aikin Hajji.
Ya ce a aikin Hajjin shekarar da ta gabata, Sarkin Gaya, Alhaji Dr Abdulkadir Ibrahim, shi ne ya jagoranci tawagar alhazan Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, tare da al’ummar Masarautar Rano, na bayyana farin cikin su da naɗin sarkin tare da godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa karramawar da yayi musu.
