Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, tare da sauran gwamnonin jam’iyyar APC masu yin wa’adi na farko, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, tare da amincewa da ci gaba da aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda har bayan zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwar bayan taron da gwamnonin su 15 suka gudanar a Birnin Kebbi, wadda gwamnan jihar ta Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu, ya karanta, gwamnonin jihohin sun bayyana goyon bayansu ga takarar wa’adi na biyu ta Shugaba Tinubu.
Gwamnonin sun ce suna sane da irin ƙalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa, amma sun bayyana cewa matakan suna da muhimmanci domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, jawo masu zuba jari, bunƙasa samar da kayayyaki da kuma ƙarfafa tsaro.
Sun kuma buƙaci ‘yan Najeriya su yi haƙuri tare da kallon ƙalubale a matsayin na ɗan lokaci, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa sauye-sauyen za su haifar da ci gaba mai ɗorewa, wadata da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa gwamnonin sun kuma nuna damuwa kan matsalolin ta’addanci da ƴan fashi da makami da garkuwa da mutane da hare-haren makarantu, tare da yin alƙawarin ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
