
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shugaban Amurka, , ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ta ƙare, bayan sabon rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin sakamakon hare-haren da Iran ta kai kan wasu jiragen ruwa a mashigin ruwa na Hormuz.
Trump ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙasashen ƙawancen NATO, inda ya ce a ganinsa babu wata ma’ana a ci gaba da tattaunawa da Iran, duk da cewa ya ce masu shiga tsakani za su iya ci gaba da yunƙurin sasanta rikicin idan suka ga dama.
Mashigin Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen safarar ɗanyen mai da sauran kayayyaki a duniya, ya sake zama cibiyar rikici.
Iran ta dage cewa ita ce ke da ikon tsara yadda jiragen ruwa za su rika wucewa, tare da neman a biya kuɗin zirga-zirga da kuma barazanar kai hari ga duk jirgin da bai bi tsarin da ta shimfiɗa ba.
Rahotanni sun ce hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa sun sa Amurka ta kai hare-hare kan wurare da dama a Iran, ciki har da cibiyoyin kariyar sararin samaniya da wasu sansanonin soji. A martaninta, Iran ta ce ta kai hare-hare kan wasu sansanonin sojojin Amurka a ƙasashen Kuwait da Bahrain.
Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Iran sun kuma ba da rahoton jerin hare-hare a yankunan da ke kusa da mashigin Hormuz, da suka haɗa da tsibirin Qeshm da biranen Sirik, Bandar Abbas da Bushehr.
Haka kuma an ce wani jami’in rundunar Revolutionary Guards ya rasa ransa a kudu maso yammacin ƙasar.
A nata ɓangaren, rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta ce ta kai hare-hare kan fiye da wurare 80 da suka haɗa da cibiyoyin kariyar sararin samaniya, na’urorin sa ido da kuma ƙananan jiragen ruwa na dakarun Revolutionary Guards, domin rage ƙarfin Iran na kai hare-hare kan jiragen kasuwanci.
A sakamakon kalaman Trump da ci gaba da rikicin, farashin ɗanyen mai ya ƙaru da kusan kashi biyar cikin ɗari, yayin da masana ke nuna damuwa kan tasirin da rikicin zai iya yi ga tattalin arzikin duniya.
Haka kuma, hukumomin tsaron teku sun tabbatar da cewa wasu jiragen ruwa uku sun fuskanci hare-hare a kusa da mashigin Hormuz, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin ƙasashen duniya game da tsaron hanyoyin safarar kayayyaki.
Sai dai Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar fahimtar juna da suka cimma a baya, bayan da Washington ta sake kakaba takunkumi kan fitar da ɗanyen man Iran zuwa kasuwannin duniya.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa rikicin na iya ƙara tsananta idan ba a samu sabuwar yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka tare da ƙasashen yankin Gulf ba.
