Zamfara Ta Amince da Biyan Alawus ga Mambobin NYSC Masu Bautar Ƙasa a Jihar
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan alawus ga mambobin National Youth Service Corps (NYSC) da ke gudanar da aikin bautar ƙasa a faɗin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na inganta walwala da jin daɗin mambobin NYSC da ke bayar da gudunmawa wajen ci gaban Zamfara.
Sanarwar ta ce amincewar ta shafi dukkan mambobin NYSC daga Batch A Stream I da II zuwa Batch C Stream I da II.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin nuna godiya ga kishin ƙasa, jajircewa da kuma gudunmawar da matasan da suka kammala karatun jami’a ke bayarwa a fannoni daban-daban, ciki har da ilimi, lafiya, noma da sauran muhimman sassa na ci gaban jihar.
Haka kuma, Gwamna Dauda Lawal ya umarci Ofishin Akanta Janar na jihar da ya kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin fara aiwatar da biyan alawus ɗin cikin tsari tare da bin ƙa’idojin da aka gindaya.
Gwamnatin Zamfara ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da bullo da shirye-shiryen da za su tallafa wa mambobin NYSC, tare da samar musu da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da aikin bautar ƙasa cikin sauƙi da inganci.
