Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce horaswar da rundunar sojin ruwan Najeriya ke bai wa jami’anta na taimakawa wajen samar da ƙarin ƙwararrun jami’an tsaro da za su inganta ayyukan rundunar da kuma bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye jami’an rundunar sojin ruwan Najeriya da suka kammala horo daban-daban a Kwalejin Harkokin Kayan Aiki ta Rundunar Sojin Ruwa da ke Dawakin Tofa.
Da yake taya waɗanda suka kammala karatun murna, Gwamna Yusuf wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Murtala Sule Garo ya ce nasarar da daliban sojojin suka samu ta samo asali ne daga jajircewa, da’a da kuma sadaukar da kai da suka nuna wajen neman ilimi da ƙwarewa a yayin horon.
Ya kuma bukace su da su ci gaba da riƙo da kyawawan ɗabi’u na mutunci, biyayya, gaskiya da kishin ƙasa, tare da amfani da ilimin da suka samu wajen kare martabar ƙasa da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa tun da farko, Kwamandan Kwalejin, Commodore A. A. Madawaki, ya yabawa ɗaliban bisa kyawawan ɗabi’a da suka nuna a lokacin horaswar, tare da ƙarfafa musu gwiwa kan amfani da ilimi da ƙwarewar da suka samu wajen gudanar da ayyukansu.
