Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana farin cikinsa da sakin masu yi wa ƙasa hidima, NYSC ’yan asalin jihar da aka sace a Jihar Imo.
An sace matasan ne a ranar 1 ga Oktoba yayin da suke tafiya daga Ibadan zuwa sansanonin NYSC da ke jihohin Abia da Akwa Ibom, bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kan motocin da suke ciki a yankin Umunoha da ke Jihar Imo.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun gudanar da wani samame da ya kai ga kubutar da masu yiwa ƙasa hidima 20 tare da wani mutum guda, an kai waɗanda aka kubutar da su asibitin hukumar DSS da ke Owerri domin duba lafiyarsu.
Gwamnatin Oyo ta ce ta samu sauƙi da jin daɗi bayan sakin matasan, tare da taya gwamnatocin Oyo da Imo da gwamnatin tarayya murna kan wannan ci gaba.
Sai dai kwamishinan yaɗa labarai na Oyo, Dotun Oyelade, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara kaimi wajen magance matsalar garkuwa da mutane da ’yan bindiga, yana mai cewa har yanzu waɗannan matsalolin tsaro na ci gaba da addabar sassan ƙasar.
