Hukumar Shari’a ta jihar kano ta fara rangadin tashoshin mota da kasuwanni, domin ƙarfafa alaƙar aiki da masu ruwa da tsaki, tare da wayar da kan jama’a kan tsafta da hanyoyin magance matsalolin da ke damun al’umma.
Tawagar hukumar ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta kai ziyara tashar motar kano Line da ke na’Ibawa, kasuwar sayar da kayan marmari ta na’Ibawa da kuma kasuwar sayar da magunguna ta Ɗangoro.
Da yake jawabi kan dalilin rangadin, Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce sun yi amfani da ziyarar ne wajen faɗakar da al’ummomin da ke tashoshin mota da kasuwannin, musamman ganin yadda wuraren ke haɗa mutane daban-daban, domin ƙara tabbatar da tsafta da zaman lafiya.
A nasa ɓangaren, wakilin shugaban hukumar sufuri ta Kano Line, Haladu Musa, da Manajan Daraktan Cibiyar sayar da magani ta Kanawa da ke Ɗangoro, Usaini Labaran Zakari, sun yabawa hukumar bisa ziyarar, tare da tabbatar da aniyar yin amfani da shawarwarin da aka ba su.
Haka kuma, Sarkin kasuwar kayan marmari ta Na’Ibawa, Mallam Abubakar Adam, da Sakataren ƙungiyar kasuwar, Adamu Muhammad, sun ce za su aiwatar da abubuwan da suka koya, yayin da Kwamishina na ɗaya na hukumar, Gwani Muhammad Hadi Yakasai, ya buƙaci shugabannin kasuwanni da tashoshin mota su riƙa tausayawa na ƙasa da su domin samun ci gaban da ya dace.
