Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wani shiri na musamman wanda zai taimakawa ɗaliban makarantun sakandare jihar, wajen zaɓen fannonin karatu da sana’o’in da suka dace, gabanin rubuta jarabawar shiga manyan makarantu ta UTME.
Gwamnan, wanda sakataren gwamnatin jihar ya wakilta, ya ce shirin zai taimaka wajen inganta tsarin bai2a ɗalibai shawarwari a makarantu, tare da ƙarawa malaman da ke kula da ɓangaren ilimi da ƙwarewar da za su jagoranci ɗalibai wajen zaɓen fannonin karatu da sana’o’in da suka dace da burinsu.
Gwamna Abba ya bayyana cewa samar da azuzuwa da malamai kaɗai ba zai wadatar wajen inganta ilimi ba, inda ya ce akwai buƙatar ɗalibai su fahimci ƙwarewa, baiwar su, abubuwan da suke sha’awa da kuma damar da ake da ita ta fuskar sana’o’i kafin su zaɓi fannin karatu ko makarantar gaba da sakandaren da za su shiga.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da fifiko ga harkar ilimi, ta hanyar inganta gine-ginen makarantu, ɗaukar malamai aiki, bayar da tallafin karatu da samar da kayan koyo.
Gwamna Yusuf ya kuma buƙaci masu ba da shawarwari a makarantu, su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da haƙuri, yayin da ya buƙaci iyaye su taimakawa ‘ya’yansu wajen zaɓen sana’o’i da fannin da suke san karanta maimakon tilasta musu abin da suke so.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na shawartar ɗalibai da su dage da karatu, su nemi shawarwarin ƙwararru tare da yin zaɓin da ya dace da burinsu, maimakon bin ra’ayin abokai, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su tabbatar da shirin ya amfani ɗalibai a dukkan ƙananan hukumomi 44 na Kano.
