Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Ubandoman Kano hakimin Takai, Alhaji Ibrahim Sani Gaya, wanda ya rasu yana da shekaru 100 a duniya.
Marigayin na daga cikin manyan masu riƙe da sarautun gargajiya mafi daɗewa a jihar Kano, inda ya shafe shekaru 67 yana riƙe da sarautarsa, tare da bayar da gudunmawa wajen jagoranci da hidimtawa al’ummar yankinsa.
Gwamna Abba ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai mutunta al’adar gargajiya, wanda tsawon shekarun da ya yi yana kan sarauta suka taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kiyaye al’adun jihar Kano.
Gwamnan ya ce rasuwar tasa babban rashi ne ga al’ummar Takai, masarautar Kano da Kano baki ɗaya, musamman duba da ƙwarewa da gudunmawar da ya bayar wajen jagoranci na tsawon shekaru da dama.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Marigayin kuma babban yaya ne ga tsohon gwamnan Kano, kuma tsohon sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.
