Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar da su ziyarci ofisoshin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke yankunansu, domin tabbatar da ganin al’umma sun karɓi dukkan katunan zaɓen su na dindindin musamman iyaye mata.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin rabon tallafin naira dubu 50-50 ga mata dubu 5,200 da aka zaɓo daga ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole, duba da yadda dubban mutanen da suka yi rajista da INEC, musamman mata, ba su karɓi katunan zaɓensu ba, inda ya cewa tuni ya tuntuɓi ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta Kano , da shugabancin ƙungiyar ƙananan hukumomi ta ƙasa ALGON, domin tabbatar da aiwatar da umarnin yadda ya kamata.
Gwamna Abba ya buƙaci mata da matasan da suka kai shekara 18 zuwa sama da su je su karɓi katunan zaɓensu, su adana su a wurare masu aminci, tare da amfani da su a zaɓen 2027.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa a yayin rabon tallafin, gwamnan Yusuf ya bayar ds kyautar kekunan guragu na mata biyu masu buƙata ta musamman wadanda baya su ke amfani da babura masu ƙafa uku, zuwa kekunan lantarki domin sauƙaƙa musu zirga-zirga.
