Bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya tabbatar da soke babban taron jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar ya shirya gudanar da taro a Abuja.
A wata sanarwa da Shugaban kwamitin, Sanata Mao Ohuabunwa, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa za a gudanar da taron ne ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026, da misalin karfe 2:00 na rana a Abuja.
- PDP Ta Bayyana Dalilin Fara Karɓar Gudunmawar Kuɗi Daga ’Ya’yan Jam’iyya
- PDP Ta Bayyana Dalilin Fara Karɓar Gudunmawar Kuɗi Daga ’Ya’yan Jam’iyya
“Ana gayyatar dukkan mambobin Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyarmu ta PDP zuwa wani muhimmin taro da za a gudanar ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026, da karfe 2:00 na rana a adireshin 1, Sabo Ago Street, LifeCamp, Abuja.” Inji sanarwar
Ohuabunwa ya kuma jaddada cewa wannan ne kadai BoT da Kwamitin Rikon Kwarya na Jam’iyyar karkashin jagorancin Abdulrahman/Anyanwu ya amince da shi, bisa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da kuma tabbatarwar Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Wannan shi ne kadai Kwamitin Amintattu da aka amince da shi bisa hukuncin kotu. Saboda haka a yi watsi da duk wani kira ko sanarwa da ke neman kiran wani taron BoT daban.”
Shugaban BoT din ya kuma bayyana cewa mambobin da aka sanar da su ne kawai za a tantance su domin halartar taron, tare da gargadin cewa duk wanda ba memba ba ya nisanci wurin taron.
