Alƙalin babbar Kotun Tarayya me lamba Ɗaya da ke jihar Kano Mai shari’a S.M. Shuaibu, ya yankewa wasu mutane uku da aka samu da laifin cin zarafin yara hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidanyari, ba tare da zaɓin tara ba.
Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa, NAPTIP, ita ta shigar da karar wanda aka fara saurara tun a watan Agustan 2025.
Waɗanda aka yankewa hukunci sun haɗa da Jibrin Adamu, maishekaru 67, mazaunin Hotoro Danmarke, Muhammadu Kanta, maishekaru 65, da kumaIshaya Hassan, maishekaru 40, dukkansumazaunajihar Kano.
An same su da laifin ɗauko mutane, musamman ƙana nan yara mata, domin cin zarafinsu.
da yake karin haske mai magana da yawun Hukumar Muhammad Habib ya bayyana cewa hukuma tasu dama ta dade tana bibiyar mutanenan bayan shigar musu da korafe korafe akan su.
wakilinmu Khalil Ibrahim Yaro ya rawaito cewa Hukumar NAPTIP tabbatar da cewa zata cigaba da zage damtse wajen ganin ta dakile safarar mutane a jihar kano dama kasa baki daya.
