Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya amince cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta kai ga magance matsalar wutar lantarki a Najeriya ba, duk da alƙawarin da ya yi gabanin zaɓen 2023.
Mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yana mai cewa gwamnatin na ci gaba da ɗaukar matakan gyara ɓangaren wutar lantarki.
Alake ya ce gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin shawo kan matsalolin kuɗi da sauran ƙalubalen da suka daɗe suna kawo cikas ga samar da ingantacciyar wutar lantarki a ƙasar.
Ya bayyana cewa Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta 2023 ƙasa da makonni biyu bayan hawansa mulki, wadda ta bai wa gwamnatocin jihohi damar samarwa da rarraba wutar lantarki a yankunansu.
A cewarsa, jihohin Legas, Enugu, Abiya, Oyo, Kaduna da Neja na daga cikin waɗanda suka fara amfani da dokar wajen inganta harkokin wutar lantarki.
Sai dai Alake ya jaddada cewa duk da matsalolin da ake fuskanta, Shugaba Tinubu bai yi watsi da alƙawarin da ya ɗauka na inganta wutar lantarki a Najeriya ba.
