Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta yi watsi da takarar Aminu Abdulsalam Gwarzo na jam’iyyar NDC a zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2027 ba.
Wani babban jami’in hukumar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa INEC ta tantance tare da amincewa da takarar Gwarzo, sai dai ba za ta iya wallafa sunansa ba saboda umarnin wucin gadi da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta bayar a ranar 27 ga Oktoba.
A cewar jami’in, umarnin kotun ya shafi wallafa sunayen ɗan takarar gwamnan Kano da mataimakinsa na jam’iyyar NDC.
Bayanin na zuwa ne bayan da sunayen Gwarzo da mataimakinsa ba su bayyana a sabon jerin sunayen ƴan takarar da INEC ta fitar a ranar Asabar ba.
Jami’in ya jaddada cewa rashin bayyana sunayensu ba yana nufin hukumar ta ƙi amincewa da takararsu ba ne, illa bin umarnin kotu har sai an yanke hukunci kan batun.
