Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON ta ce maniyyatan ƙasar kimanin 50,000 ne za su suke farali a wannan shekara ta 2026.
Mataimakiyar darakta a sashen yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ce ta bayyana haka a hirarta da BBC.
A yau ne dai ake fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki.
Fatima Sanda Usara ta ce tuni hukumarsu ta kammala dukkan shirye-shirye da suka kamata don gudanar da jigilar maniyyatan cikin nasara.
A baya dai ana yawan samun jinkiri a aikin jigilar alhazan Najeriyar a duk shekara, wanda hakan kan sa wasu alhazan su gaza samun damar sauke faralin, sai dai Fatima, ta ce tuni suka ɗauki mataki kan lamarin.
