Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDiplomasiyya: UAE ta dakatar da baiwa 'Yan Najeriya Visa

Diplomasiyya: UAE ta dakatar da baiwa ‘Yan Najeriya Visa

Date:

Hukumar shige da fice ta kasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce ta dakatar da bai wa ‘yan Najeriya Visa, saboda matsalolin da suka shafi diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

 

A wata sanarwa da suka aike wa kamfanonin shirya tafiye-tafiye a Najeriya ranar Juma’a, hukumomin kasar ta UAE sun ce ”duk takardun neman izinin biza da aka cike an dakatar da su yanzu”.

 

Jaridar The Cable a ta ruwaito gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duk wadanda suka cika takardun neman Visa za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.

 

Ta kuma ce ”kin amincewar ya shafi kowanne dan Najeriya, dan haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu”.

 

Ta kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba ne zuwa lokacin da za ta sulhunta da gwamnatin Najeriya.

 

Wannan mataki na zuwa ne wata guda bayan da kasar ta UAE ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga ‘yan kasa da shekara 40, lamarin da ya shafi ‘yan Najeriya da na wasu kasashen.

 

Ko a shekarar 2021 ma dai ƙasashen biyu sun shafe watanni masu yawa suna ce-ce-ku-ce game da harkar sufurin jiragen sama

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...