24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBuhari zai tafi kasar Koriya ta Kudu yau Lahadi

Buhari zai tafi kasar Koriya ta Kudu yau Lahadi

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Koriya ta Kudu domin halartar taron duniya na farko kan fasahar sarrafa tsirrai.

 

Buhari zai kuma gabatar da jawabi ga taron na kwana biyu, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Gwamnatin Koriya ta Kudu suka shirya.

Taron wanda zai mayar da hankali kan samar da riga-kafi zai gudana ne ranar 25 zuwa 26 ga wata Oktoba, da muke ciki.

 

A lokacin taron, masana da kamfanoni hada magunguna za su gabatar da jawabai kan samar da riga-kafi daga tsirrai da makomar fannin.

 

Najeriya na cikin kasashen Afirka shida da WHO da Tarayyar Turai (EU) ta bai wa goron gayyatar taron tun a watan Fabrairu a birnin Brussels na kasar Belgium.

 

A lokacin taron, Shugaba Buhari zai gana da Shugaba Yoon Suk-yeol kan wasu batutuwan hadin gwiwa da Najeriya za ta amfana.

 

Zai kuma yi tattaunawa da wasu bangarori kan hanyoyi da batutuwa da Najeriya za ta amfana ta fannin kasuwanci da zuba jari da sauransu.

 

’Yan rakiyar shugaban kasa sun hada da ministocin Lafiya, harkokin waje, kasuwanci da zuba jari, man fetur, da harkokin waje.

Sai kuma gwamnonin jihar Katsina da Neja da sauran jami’an gwamnati.

Latest stories