Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ba ta taɓa neman wannan kuɗi a matsayin sharadin sakin matar ba.
Mai magana da yawun rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya ce matar mai suna Nwosu Chikamso Jennifer, an kama ta ne yayin gudanar da bincike kan wasu kashe-kashe da ake zargin ƙungiyoyin asiri ne suka aikata a birnin Awka.
Ya ce binciken ya nuna cewa ɗan’uwanta, Nwosu Kenechukwu, ya zama wanda ake nema domin yi masa tambayoyi kan waɗannan laifuka, kuma matar ta taimaka masa wajen kauce wa kama.
Rundunar ta ce daga bisani an saki Jennifer bisa beli, bayan ta amince za ta bada haɗin kai ga masu bincike tare da taimakawa wajen gano inda ɗan’uwanta yake.
’Yan sandan sun kuma yi watsi da zargin cewa an nemi 600,000 ko wani kuɗi a matsayin sharadin sakin ta, suna mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.
Rundunar ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da sauran jama’a da su tabbatar da irin waɗannan zarge-zarge masu muhimmanci daga hukumomin da abin ya shafa kafin yaɗa su.
