Shugabar jami’ar Northwest a nan Kano Farfesa Amina Salihi Bayero ta gargadi sabbin daliban da jami’ar ta bawa gurbin karatu da su guji afkawa duk wani nau’i na laifi da zai sa jami’ar ta kore su baki daya.
Daga cikin dokokin da jami’ar ta sanya akwai kauracewa, duk wani nau’i na saba dokokin jarrabawa, da kauracewa shiga duk wata kungiya da jami’ar bata aminta da ita ba, da kuma samun sakamako mai kyau a karatu.
A tattaunawar ta da wakilinmu Ibrahim Hassan Bako Dambatta jim kadan bayan rantsar da sabbin daliban a Juma’ar nan, farfesa Amina ta ce jami’ar ba zata lamunci ganin dalibai suna karya duk dokokin da jami’ar ta shimfida ba.
Suma wasu daga cikin daliban da wakilin namu ya tattauna da su bayan karbar rantsuwar fara karatu, sun bayyana gamsuwar su bisa yadda jami’ar ta karbe su cikin tsari, tare da daukar aniyar bada himma yayin karatun su a jami’ar.
Sama da dalibai 7,900 jami’ar ta karba a zango karatu na shekarar 2025 da suka fara karatu a farkon makon nan, wanda ya zama karo na 13 kenan da jami’ar ke bikin rantsar da sabbin dalibai makamantan wannan.
