
Aminu Abdullahi Ibrahim
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da hukumar zabe INEC daga amincewa da tarukan da jam’iyar ADC tsagin su David Mark suka gudanar a matakin jihohi.
Da take yanke hukuncin mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ce ikon gudanar da tarukan jam’iyar na jihohi hakki ne na shugabanin jiha ba tarayya ba.
Kotun ta kara yanke hukunci cewa wa’adin shekaru hudu na kwamitocin Jiha na ADC da kwamitocin zartaswa na Jiha zasu ci gaba da kasancewa, har zuwa lokacin da za a gudanar da tarukan jiha da kuma kiran taron kasa.
Mai shari’a Abdulmalik ta kuma tabbatar da cewa ba kundin tsarin Mulkin Najeriya ko na jam’iyyar da suka ba da dama ga kwamitin rikon kwarya ko wucin gadi na kwamitin zartaswa na kasa, wanda David Mark ke jagoranta, don naɗa kwamitoci domin gudanar da tarukan jiha.
