Gidan talabijin na JKD da ke Kaduna, mallakin Ambasada Yusuf Mamman, ya maka mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabiru Masari, da rundunar ’yan sandan Najeriya a kotu bisa zargin take haƙƙin ma’aikatansa.
Kamfanin JKD Multimedia Limited, mai gudanar da JKD Television da Hamada Radio Network, ya shigar da ƙarar a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ranar 19 ga Oktoban 2026.
Kamfanin na neman diyyar naira miliyan 15, tare da umarnin kotu na hana waɗanda ake ƙara sake shiga wuraren aikinsa ba bisa ƙa’ida ba ko kama ma’aikatansa da ’yan uwansu.
Ƙarar ta biyo bayan zargin kutsen jami’an ’yan sanda dauke da makamai cikin harabar kamfanin ranar 11 ga Satumbar 2026, inda aka ce sun tsare babban manajansa.
A cewar daraktar kamfanin, Aisha Yusuf Mamman, jami’an sun shiga harabar ba tare da umarnin kotu ko takardar izini ba. Kamfanin ya ce ya garzaya kotu ne bayan yunƙurin sasanta rikicin bai yi nasara ba.
Masu ƙarar sun ce matakan da ake zargin an ɗauka sun saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin kasa, duk da haka, kamfanin ya ce a shirye yake ya sasanta rikicin ta hanyar tattaunawa.
