Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an riga an sanya hannu ta yanar gizo kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin Amurka da Iran, yana mai cewa za a buɗe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz gaba ɗaya ga zirga-zirgar jiragen ruwa daga ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce jami’ai daga bangarorin biyu sun tabbatar da cewa Trump da Mataimakinsa, JD Vance, tare da babban mai shiga tsakani daga Iran kuma Kakakin Majalisar Dokokin kasar, Mohammad Bagher Ghalibaf, sun sanya hannu kan yarjejeniyar ta hanyar yanar gizo.
Abubuwan da aka sani game da yarjejeniyar
Har yanzu ba a fitar da cikakkun bayanan yarjejeniyar ba, amma Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ta ce yarjejeniyar za ta kawo karshen fada a dukkan bangarori, ciki har da rikicin da ke gudana a Lebanon, tare da kawo karshen katangar ruwa da Amurka ta kakaba wa tashoshin jiragen ruwan Iran.
Bangarorin biyu sun ce za a ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da kuma batun sassauta takunkuman tattalin arziki a cikin kwanaki 60 bayan sanya hannu a hukumance a Switzerland ranar Juma’a.
Trump ya ce mashigar Hormuz za ta kasance “a bude ga kowa”, yayin da Vance ya ce ba za a karbi kudin wucewa daga jiragen ruwa ba a lokacin tattaunawar.
Wani babban jami’in Iran ya shaida wa Reuters cewa Amurka ta amince da sakin dala biliyan 25 na kadarorin Iran da aka rike tare da sassauta takunkumin man fetur na wani lokaci.
Sai dai Vance ya musanta hakan, yana cewa babu ko dala daya da aka saki daga kadarorin Iran kuma babu wani sassaucin takunkumi da Amurka ta bayar zuwa yanzu.
Ya kara da cewa yarjejeniyar takarda ce ta gaba ɗaya mai kusan shafi daya da rabi, kuma za a iya bayyana cikakkun bayananta nan gaba kadan.
Martanin Iran
Kafin sanya hannu kan yarjejeniyar, Ghalibaf ya wallafa sako a shafinsa na X inda ya ce Iran ta dauki “babban mataki zuwa ga nasara” bayan abin da ya kira tarihi na juriya da kasar ta nuna a yakin da Isra’ila da Amurka.
Kafofin yada labaran Iran sun kuma ce tun bayan sanar da yarjejeniyar, akalla tankokin dakon man fetur guda uku na Iran da wasu jiragen ruwa masu dauke da kayayyaki sun ratsa mashigar Hormuz.
Shugaban kungiyar ma’aikatan jiragen ruwa ta Iran, Saman Rezaei, ya ce har yanzu dawo da zirga-zirga yadda take kafin yakin ba abu ne mai sauki ba, yana mai cewa akwai bukatar zaman lafiya mai dorewa da kuma tafiya ba tare da afkuwar wani sabon rikici ba.
Ya kuma ce kusan ma’aikatan jiragen ruwa 22,000 ne suka makale a yankin Tekun Fasha tsawon kusan watanni hudu.
Martani a Amurka
Vance ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wadda za ta amfani bangarorin biyu, yana mai cewa za ta kasance “nasara ga al’ummar Amurka”.
Trump kuwa ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Amurka za ta biya Iran kudi, yana mai cewa irin wadannan rahotanni “labaran karya ne”.
Sai dai wasu ‘yan siyasar jam’iyyar Democrat sun soki yarjejeniyar, suna cewa ya kamata a yi karin bayani kan cikakkun sharuddan da ke cikinta kafin a amince da ita.
Isra’ila da Lebanon
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce dakarun kasarsa za su ci gaba da zama a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Iran.
Wasu mambobin gwamnatin Isra’ila ma sun bayyana cewa ba sa ganin yarjejeniyar za ta hana kasar ci gaba da daukar matakan soji kan kungiyar Hezbollah.
A Lebanon kuwa, hare-haren Isra’ila sun yi sanadin mutuwar akalla mutum guda a ranar Litinin, yayin da dubban mutane da suka rasa matsugunansu ke ci gaba da komawa gidajensu da yakin ya lalata.
