Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiCBN ya bukaci bankunan kasuwanci na Kano su shiga tsarin bada bashin...

CBN ya bukaci bankunan kasuwanci na Kano su shiga tsarin bada bashin manoma.

Date:

Babban bankin kasa CBN ya bukaci bankunan kasuwanci a jihar Kano da su shiga cikin tsarin nan na bada bashin noma domin bunkasa fannin noma a kasar nan.

Shugaban bankin reshen jihar Kano Alhaji Umar Ibrahim Biu ne yayi wannan roko a wajen liyafar cin abincin dare tare da bada kyautuka na shekarar 2023 da bankunan suka shirya a larabar nan.

Biu yace rokon ya zama wajibi duba da cewa kananan bankunan masna’antu ne kadai ke taka rawa a cikin tsarin, yace shigar bankunan cikin wannan tsari zai kara bunkasa sha’anin noma a jihar Kano

Bayanai na nuna cewar A shekarar 2023, mutane 575 ne kacal suka samu rabauta da bashin noman a nan Kano da kudin da aka bayar a matsayin bashin ya kai naira miliyan 94 da dubu 289

Tsarin dai an kirkireshi ne domin saukakawa manoma samun bashi, amma karancin shigar bankunan kasuwanci cikinsa na zama wani babban tarnaki, tare da takaita yawan manoman da zasu amfana karkashin tsarin.

A don haka Alhaji Ibrahim Biu shugaban babban bankin kasa CBN reshen Kano ya shawarci masu sha’awar karbar bashin noman da su tuntubi cibiyoyyin kudi dake kusa dasu domin karbar takardar neman bashin kyauta.

Latest stories

Related stories