Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMahamat Deby ya lashe zagayen farko na zaben shugaban kasar Chadi.

Mahamat Deby ya lashe zagayen farko na zaben shugaban kasar Chadi.

Date:

Sakamakon zaɓen shugaban kasa a Chadi ya bayyana jagoran mulkin Sojin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na zaɓen wanda ke nuna yiwuwar ya iya tsawaita wa’adin mulkin iyalan gidan Deby na wasu karin shekaru.

Zaɓen na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin riƙon ƙwarya na shekaru 3 da Chadi ta fuskanta tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno a fagen daga wanda ya baiwa ɗansa Janar Mahamat Deby damar jan ragamar kasar mai fama da rikice-rikice baya ga ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta ANGE ta fitar ya nuna yadda Mahamat Deby ya lashe jumullar kashi 61.3 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa yayinda Firaministan ƙasar Success Masra ya lashe kashi 18.53.

Kowanne lokaci daga yanzu ne ake dakon kotun kundin tsarin mulki ta tabbatar da sahihancin zaɓen.

Sai dai tuni Firaminista Masra ya ƙalubalanci sakamakon wanda ya bayyana da marar inganci.

A bangare guda tuni Shugaba Mahamat Deby Itno ya gabatar da jawabin kai tsaye ta gidan talabijin tare da godewa al’ummar ƙasar kan zaɓensa baya ga shan alwashin samar da yanayi mai inganci ga al’umma.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...