Dubban alhazai sun gudanar da addu’o’i a Dutsen Arafat da ke kusa da birnin Makka a yau Talata, yayin da aikin Hajjin bana ya kai mataki mafi muhimmanci.
Tun da sanyin safiya, mahajjata sanye da fararen harami suka rika karatun Alƙur’ani da addu’o’i a dutsen mai tsawon mita 70, wurin da aka yi imanin Annabi Muhammad (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta bankwana.
Masu aikin sa kai sun rika rabon ruwan sha, lema da kayan abinci ga dubban mahajjatan da suka nufi Dutsen Arafat.
Wani mahajjaci ɗan kasar Masar mai suna Ahmoud Abou Elezz ya bayyana jin dadinsa yayin isa wurin karo na farko.
Ya ce: “Abu ne da ba zan iya bayyana shi da kalmomi ba.”
Fiye da mutum miliyan 1.5 daga sassa daban-daban na duniya ne suka halarci Hajjin bana duk da rikice-rikicen da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da yaƙin Iran da Isra’ila da kuma hare-haren da ake kaiwa Gaza, Lebanon da Syria.
Hukumomin Saudiyya sun ce yawan mahajjatan da suka zo daga ƙasashen waje a bana ya fi na shekarar 2025.
Hajji na ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, kuma wajibi ne ga duk Musulmin da suke da hali su yi shi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu.
Saboda tsananin zafi da ya kai kusan digiri 44 a Makka cikin kwanakin nan, hukumomin Saudiyya sun shawarci mahajjata da su yawaita shan ruwa tare da kare kansu daga rana.
Bayan kammala zaman Arafat, ana sa ran mahajjata za su kwana a Muzdalifa kafin su tattara duwatsu domin gudanar da jifan shaidan a Mina daga ranar Laraba.
