Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari Zai Tafi Kasar Guinea-Bissau A Yau.

Buhari Zai Tafi Kasar Guinea-Bissau A Yau.

Date:

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Laraba zai tashi zuwa birnin Bissau na kasar Guinea Bissau da ke yammacin Afirka.

 

Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya fitar, tace Buhari zai amsa goron gayyatar da shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissolo Embalo ya yi masa na bikin na musamman a fadarsa, wanda zai hada da kaddamar da wata hanya mai sunan Buhari a babban birnin kasar.

 

Bikin na kwana guda zai bayyana irin rawar da shugaba Buhari ya taka a gabar tekun Yamma, musamman a kasar Guinea Bissau, da nasiha da karfafa gwiwar shugabanni akai-akai kan kyawawan dabi’u na zaman lafiya, hada kai da siyasa, dai-daito da kuma karfafa tattalin arziki mai karfi da zai samar da ci gaban kasa baki daya.

 

A ziyarar, Buhari da tawagarsa za su halarci taron bisa rakiyar karamin ministan harkokin kasashen waje Ambasada Zubairu Dada, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...