Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN ya ce daga yanzu N,100,000 mutum zai iya cirewa daga bankinsa...

CBN ya ce daga yanzu N,100,000 mutum zai iya cirewa daga bankinsa a sati

Date:

Babban bankin kasa CBN ya ce sabon tsarin amfani da kudi da aka shigo dashi aya yanzu ya ce mutum zai iya cure N100,000 kawai daga bankinsa cikin mako guda.

 

Wanna na kunshe cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar ranar Talata.

 

Ta cikin sanarwar CBN ya takaita yawan kuɗaden da yan Najeriya za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.

 

Sabbin matakan da CBN ya fito da su sun Hadar da.

 

  1. Yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

 

Idan mutum na son cire kuɗin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum, sai kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.

 

  1. Duk wanda ya je banki cire kudin da suka haura naira 50,000 da caki na banki da wani ya rubuta masa, to ba za a ba shi kudin ba.

 

Yayin da dokar cire kuɗin da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da caki a tsakanin bankuna daban-daban tana nan a yadda take.

 

  1. Yawan kudin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cire kudi ta ATM a sati kuwa shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a ranar naira 20,000 ne kacal.

 

  1. Takardun kudin naira 200 kawai bankuna za su dinga lodawa a cikin na’urar ATM.

 

  1. Idan a wajen masu amfani da na’urar POS ne kuwa, naira 20,000 ce yawan kudin da mutum zai iya cirewa.

 

A yayin ƙaddamar da sabbin kuɗaɗen ranar 23 ga watan Nuwamban 2022, Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.

 

Dama tun a watan Oktoban da ya gabata CBN ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗen ƙasar, tare da umartar mutane da su mayar da tsofaffin kudaɗen banki don sauya musu da sababbi.

 

CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.

Latest stories

Related stories