Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniYau shekaru 13 da rasuwar Talban Bauchi Dr Ibrahim Tahir

Yau shekaru 13 da rasuwar Talban Bauchi Dr Ibrahim Tahir

Date:

Muhammad Bello Dabai

 

A duk rana mai kamar ta yau, wato 8 ga watan Disambar kowacce shekara, jimamin rashin Talban Bauchi, Dr Ibrahim Tahir, na sake zama sabo.

 

A makamanciyar ranar ce, a shekarar 2009, aka wayi gari da labarin rasuwarsa, bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.

 

Ga yawancin al’ummar yankin arewacin Najeriya, babu ko shakka wannan batu zai jangwalo musu tsohon ciwo, la’akari da gudunmawar marigayin wajen cigaban yankin ta fuskoki da dama.

 

Shi dai ya kasance malamin addini, Dan siyasa mai ra’ayin rikau, masanin zamantakewa, kuma marubuci.

 

An dai haifi Dr Ibrahim Tahir, a kauyen Tafawa Balewa dake jihar Bauchi, kuma yayi karatun Firamare a makarantar Kobi.

 

A shekarar 1954 ne ya shiga kwalejin Barewa, wadda ya kammala a 1958, sannan ya sami gurbin karatu a jami’ar Cambridge dake London, wadda gwamnatin lardi ta dauki nauyinsa.

 

A nan ya kammala digirinsa na farko zuwa digirin digirgir a sashin nazarin zamantakewa.

 

A shekarar 1967, marigayin ya sami aikin koyarwa a jamiar Ahmadu Bello dake Zaria, inda a nan ya kirkiro wata kungiyar dabbaka manufofin Sardauna, wato Gamji Club.

 

Irin wannan, da dangoginsu, ya sanya a lokacin ake masa kallon mai ra’ayin rikau, domin bayan shudewar jamhuriya ta farko, shine ya jagoranci tafiyar dabbaka al’adu da manufofin Arewa, kuma sirrin armashinta shine, hadewarsa da wata tawagar kundumbala, wato Kaduna Mafia, wadanda suka kunshi ma’aikatan gwamnati, sojoji, kwararru, malamai da sauransu, kuma manufar su bata wuce Fifita arewa da bukatun al’umar ta ba.

 

A sha’anin siyasa. Marigayi Ibrahim Tahir na daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar NPN a 1978, wadda daga baya ya zama sakatarenta.

 

Sannan ya rike mukamin shugabancin kungiyar bunkasa cigaban yankin arewa wato NNDC, sannan daga baya ya zama ministan sadarwa.

 

Har ila yau, ya shugabanci kungiyar agajin nan ta kasa da kasa wato Red Cross Society, reshen Najeriya.

 

Sakamakon tasirin addini, da na turawan mulkin mallaka, ana kallon kwarewa a sanin yaren Larabci da turanci a yankin arewa, ko ma Najeriya baki daya a matsayin gwamnancewa.

 

To babu shakka, idan za’a so mutum don kwarewarsa a yaren Larabci ko Turanci, sunan Dr Ibrahim Tahir ba zai buy aba, domin zarrarsa a bangaren, yakan iya yara wadannan harsuna tamkar harshen uwa.

 

Kafin rasuwar Marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, akwai wani rubutu da yayi game da Talban Bauchin, wanda ya zayyano irin tarin baiwa da Allah yayi masa, da farin farawa ma, bayyana Marigayin yayi a matsayin wanda ya kafa masa tubalin karatu, har zuwa matakin da ya kai.

Abinda ya ja hankali a rubutun shine, inda Kyari ke labarta yadda ta kaya a lokacin rasuwar mahaifinsa. Yace sandsa Talban Bauchi yaje Borno yi masa ta’aziyya, sai da ya shafe tsawon mintuna 45 ya zuba addua da yaren Larabci.

 

Sai da ta kai Al’ummar Borno sun gamsu cewa Dr Ibrahim Tahir ya yi wa duk wani malamin addini da sake yankin fintinkau a sanin yaren Larabci.

 

A matsayinsa na malamin addini, daga irin gudunmawarv da ya bayar, akwai shahararren Littafinsa da ya rubuta mai suna Qur’an has the answers, wanda ke amsa tambayoyin tauhidi, da zamantakewa kai tsaye daga ayoyin al’qur’ani.

 

Sannan a irin littafan da ya wallafa, akwai shahararren littafin nan mai take the last imam; wanda shikuma, yam ai da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi zamantakewa, da ya hadar da batun auren mace fiye da daya, al’adun maguzanci, bautar da mata, da amfani da karfi fiye da kima.

 

A iya kalmomin dake akwai a duk yarukan duniya, ba lallai a iya kammala tattaro bayanai da su ba, wadanda zasu gamsar wajen fayyace wanene Marigayi Ibrahim Tahir.

 

Sai dai mu ce Allah ya jaddada rahama a gare shi…

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories