Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ya sa a binciki musabbabin gobara a Onitsha

Buhari ya sa a binciki musabbabin gobara a Onitsha

Date:

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya umarci a gudanar da bincike kan musabbabin faruwar wata gobara da ta hallaka mutane a kasuwar Onitsha dake jihar Anambra.

 

A sakon da ya fitar ta hannun kakakinsa Mal Garba Shehu, Buhari ya jajanta wa iyalan wadanda gobarar ta halaka, da kuma taya ‘yan kasuwar da suka tafka asara jimami.

 

Daga nan ya yi fatan samun waraka ga wadanda suka jikkata a iftila’in.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su gaggauta kai tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.

 

Bayanai sun ce gobarar ta tashi a kasuwar ne ranar Talata da misalin karfe 12:00 na rana, bayan da sinadaran da ke tattare a shaguna suka soma fashewa.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...