Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBance zan mika jami'o'in gwamnatin tarayya ga jihoji ba-Atiku Abubakar

Bance zan mika jami’o’in gwamnatin tarayya ga jihoji ba-Atiku Abubakar

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Dan takarar shugaban kasar nan a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya musanta zancen da ake yadawa cewar zai mayar da jami’o’in kasar nan hannun gwamnonin jihoji.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Paul Ibe ya fitar da yammacin ranar Litinin.

Paul ya ce sun lura an juya maganar da dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya a Legas.

Yayi dogon jawabi ne kan batun da ya shafi bangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da bangaren ke fuskanta.

Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai mika ragamar kula da jami’in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa.

“Wannan ba daidai ba ne don bai fadi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa” in ji shi.

Ya ce abin da Atiku Abubkar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami’on da ke karkashinta.

A don haka batun cewa zai mika wa gwamnatocin jihohi ragamar tafiyar da jami’oi ba gaskiya ba ne.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories