Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba.
yana mai cewa dawo da shi zai iya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya a Abuja.
inda ya mayar da martani kan alƙawuran wasu ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun hamayya na dawo da tallafin idan suka lashe zaɓen 2027.
Shugaban ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da kashe kuɗaɗen da take kashewa wajen biyan tallafin man fetur ba.
