An sake ɗage zaɓen da Majalisar Dokokin Masar za ta yi domin bai wa Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ikon bayar da tallafin soja ga Saudia.
An ɗage zaman ne zuwa ranar 26 ga Oktoba domin ba wa dukkan ‘yan majalisa damar gabatar da ra’ayoyinsu da yin muhawara kan batun kafin a kaɗa ƙuri’a.
A ranar Asabar, Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya buƙaci ‘yan majalisar da su amince da baiwa gwamnatin Masar damar tallafawa Saudiyya idan ta nemi taimako wajen fuskantar hare-haren mayakan Houthi.
Masar ta shiga kawancen sojin da Saudia ke jagoranta a yaƙin Yemen tun shekarar 2015. Sai dai rawar da ta taka ta fi karkata wajen kare hanyoyin jigilar kayayyaki ta Teku maimakon shiga kai tsaye a manyan hare-haren yaƙi.
A gefe guda, wasu manyan jami’an Houthi sun gargadi Masar da kada ta shiga rikicinsu da Saudiyya.
