Jihar Kano ta samu gagarumar nasara wajen rage mace-macen mata masu ju na biyu da masu haihuwa, inda adadin ya sauka daga mutum 1,026 zuwa 570, sakamakon shirye-shiryen inganta kula da lafiyar mata da aka aiwatar a jihar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana hakan yayin taron bita kan nasarorin da ma’aikatar lafiya ta samu, musamman bangaren mata masu juna biyu, inda ya ce an horar da ma’aikatan lafiya, inganta cibiyoyin kiwon lafiya, tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancin haihuwa a asibiti.
Ya ce sabbin hanyoyin kula da zubar jini bayan haihuwa, wato E-MOTIVE, sun taimaka matuƙa wajen ceton rayukan mata, kuma idan aka ci gaba da irin waɗannan matakai, ana sa ran za a ƙara rage mace-macen da kaso tsakanin 25 zuwa 30 cikin 100 cikin shekara ɗaya da rabi masu zuwa.
Dakta Labaran yace shirin ya mayar da hankali ne kan ƙananan hukumomi 18 da suka fi fama da matsalar, inda aka ceto rayukan mata da dama ta hanyar samar musu da kulawar gaggawa da kuma ƙara ƙwarewar ma’aikatan lafiya.
