
Ƙungiyar masu noman tumatir a Najeriya ta bayyana fargabar samun ƙarancin tumatir wanda hakan zai haifar da tsadarsa a kasar, sakamokon barnar da wata tsusa da ke illart tumatirin a kasar.
Kungiyar manoman tumatir ta koka cewa tun farkon watan Maris shekarar 2025 suka fara ganin bullar fitinanniyar tsutsar timatir din da ake kira Tuta Absaluta, inda ta yiwa dumbin gonaki mummunar barna a wasu jihohin arewacin Najeriya.
A hirarsa da BBC, Alhaji Sani Danladi Yada-Kwari, shugaban kungiyar manoma timatir na jihar Kano, kuma sakataren kungiyar na kasa. Ya ce tsutsar ta yi mummunar illa a jihohin Kano da Jigawa da kuma Bauchi.
”Musamman a nan jihar Kano, ta yi mana ta’adi matuƙa duba da yadda duk wanda ya zama timatirinsa bai fara ɗibar shi ba, wanda ya dasa shi daga watan 11, watan 12 wallahi bai sami komai a gonarsa ba.”
Alhaji Sani Yada-Kwari ya ƙara dacewa ”akwai wanda ya gama aikinsa gaba ɗaya, yana tunanin zai ɗiba, timatirin ya ƙone. Wani ya je gonarsa ya ga timatir ɗin amma a kwana uku gaba ɗaya tsutsar nan ta lalata shi”
A kan haka ne ma ƴan kasuwar ke hasashen cewa a bana za a samu tsadar timatir sosai domin tsutsar ta yi illa sosai a gonaki.
Dangane da girman ɓarnar da manoman suka yi kawo yanzu kuwa, Alhaji Sani Yada-Kwari ya ce, har yanzu suna tattara alƙalumma, ”amma ina tabbatar maka a nan jihar Kano, manoma sun yi asarar da ba ta gaza naira biliyan 20 ba.”
Yanayin zafi na cikin abubuwan da ke sanya tsutsar tumatir din ta’azzara, kuma tana da wuyar magani, kasancewar ta na bijirewa maganin da ake fesa mata.
Shima sakataren kungiyar masu hada-hadar tumatir a kasuwar Ƴan Kaba, Alin Bello ya ce yanzu haka akwai ƙarancin timatir a kasuwanni saboda wannan matsala.