Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Date:

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an kashe ‘yan ƙato-da-gora aƙalla ashirin da uku, a wasu hare-hare daban-daban, da ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya suka kai musu a ƙarshen makon da ya gabata.

A jihar Borno, ana zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne suka dasa nakiyoyin da suka tashi a cikin wata mota ɗauke da ‘yan ƙato-da-gora, da aka fi sani da sibiliyan JTF, kamar yadda shugabansu ya tabbatarwa manema labarai.

Tijjanima Umar, shugaban CJTF na yankin Gamboru Ngala, ya ce motar jami’ansu na kan hanyar zuwa Maiduguri lokacin da nakiyoyi suka fashe inda suka kashe ‘yan ƙato-da-gora da yawa.

Duk da yake sojojin tarayya da ‘yan ƙato-da-gora sun ci ƙarfin mayaƙan Boko Haram da na ISWAP da suka addabi arewa maso gabashin ƙasar nan, har yanzu suna kai hare-hare jefi-jefi kan farar-hula da jami’an tsaro.

A can Sakkwato kuma, ‘yan bindiga sun yi kwanton-ɓauna kan ‘yan sibiliyan JFT, inda suka kashe 14 daga cikinsu, kamar yadda kwamandansu, Ismail Haruna ya tabbatarwa majiyarmu ta wayar tarho.

Latest stories

Related stories