Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce a shirye yake ya janye daga tikitin takararsa tare da Atiku Abubakar, domin ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kamfen a zaɓen 2027, idan farashin litar man fetur ya koma ₦600.
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today ranar Juma’a.
Tsohon gwamnan na Rivers ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ƙara jefa ’yan Najeriya cikin matsin rayuwa.
Ya ƙalubalanci shugaban ƙasar da ya tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun fara sauƙaƙa wa jama’a rayuwa, musamman wajen farashin man fetur da kuɗin sufuri.
Amaechi ya ce har ya shirya zuwa gidan mai da kansa domin tabbatar da farashin litar fetur, inda ya yi alƙawarin cewa idan ya samu ana sayar da ita kan ₦600 zuwa ranar Asabar, zai janye daga tikitin ADC tare da fara yi wa Tinubu kamfen.
Ya kuma bayyana zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin muhimmin zaɓi da zai shafi makomar ’yan Najeriya, yana mai sukar yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.
