Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta yi kira ga ’yan Najeriya da su riƙa neman shugabannin siyasa su yi bayanin ayyukansu, musamman kan matsalar tsaro, talauci da matsin tattalin arzikin da ƙasar ke ciki.
Shugaban ƙungiyar, Mamman Osuman, ne ya bayyana hakan a saƙonsa na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Osuman ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke haddasa gudun hijira, rufe makarantu, durƙushewar harkokin kasuwanci da lalacewar hanyoyin samun abin dogaro da kai.
Ya ce wasu daga cikin matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta na da alaƙa da ayyukan mutanen da aka damƙa wa ragamar shugabanci.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, shugaban ACF ya buƙaci ’yan Najeriya da suka cancanta su mallaki katin zaɓe na dindindin tare da shiga zaɓe domin zaɓar shugabannin da suke ganin sun cancanci jagorantar ƙasar.
Haka kuma, ya gargaɗi masu zaɓe da kada su dogara kawai da umarnin jam’iyyun siyasa, inda ya jaddada muhimmancin yin nazari kan tarihin ’yan takara, manufofinsu da matsalolin ƙasar kafin yanke shawarar wanda za
