Gwamnatin Kano ta ce zata yi nazari kan bukatar da gwamnatin kasar Sudan ta gabatar mata na neman izinin yin amfani da Asibitin Nasarawa na wucin gadi, a matsayin asibitin koyarwa na jami’ar El-Razi, tare da neman gwamnatin ta sama mata da fili domin gina asibitin Sudan da ofishin al’ummar Sudanawa a jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar, Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin da ya karbi bakuncin Jakadan Sudan a Najeriya, Sheikh Mohammed Abdelaal Haroon.
Murtala Garo ya ce za’a mika bukatar amfani da Asibitin Nasarawa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin yin nazari bayan samun shawarwarin kwararru, yayin da bukatar bayar da fili itama yayi alkwarin za ta samu kulawar da ta dace.
A nasa jawabin, Jakadan Sudan a Najeriya, Sheikh Mohammed Abdelaal Haroon, ya ce dangantakar Najeriya da Sudan ta dade tana da anfanar kasashen biyu, inda ya bayyana Kano a matsayin ginshikin alakar, tare da bukatar gwamnatin Kano ta amince kudurin na su domin kara karfafa hadin gwiwa musamman a fannonin lafiya da ilimi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Garo na jajantawa da mika ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Sudan kan rikicin da ke ci gaba da addabar kasar, tare da jaddada kudirin Kano na kara inganta hadin gwiwa a bangarorin lafiya, ilimi, noma, kasuwanci da musayar al’adu da kasar ta Sudan.
