Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniBarcelona za ta lashe Laliga ta bana idan tayi nasara a wasa...

Barcelona za ta lashe Laliga ta bana idan tayi nasara a wasa na gaba

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, za ta zama zakara a gasar La Liga ta kakar wasannin 2022/2023 idan har tayi nasara a wasan mako mai zuwa.

Wannan na zuwa ne bayan da Barcelona tayi nasara kan Osasuna da ci 1-0 a wasan da suka fafata a ranar Talata.

Barcelona kawo yanzu na mataki na farko a Teburin gasar da maki 82 a wasa 33 da ta fafata.

Hakan ke nuni da cewa Barcelona ta bawa Madrid ta zarar maki 14, kum a idan tayi nasara a wasa na gaba da zata buga da Espanyol kungiyar ta lashe gasar ta bana.

Yanzu haka dai Real Madrid itace ke rike da kambun gasar data lashe a kakar bara, kuma jumulla a tarihi ta lashe gasar sau 35.

Sai kuma Barcelona da ta lashe gasar sau 26, wanda idan ta lashe gasar bana to ta lashe gasar jumulla sau 27 a tarihi.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Sabbin Yan Wasa 12 da Kano Pillars ta dauka

Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars, wadda ta lashe...