Shugaban kasar Liberia George Weah ya taya murna ga Dan wasa Victor Osimhen, wanda ya taimakawa Napoli lash gasar Serie A a karon farko tin shekaru 33 da suka gabata.
Osimhen ya Kuma zama dan wasan nahiyar Afrika mafi yawan zura kwallo a wata gasa a kasar Italiya.
Wannan na zuwa ne bayan da Osimhen ya zura kwallo, a wasan da Napoli tayi nasara kan Fiorentina da ci 1-0 a karshen mako.
Kuma ya kamo tarihin yawan zura kwallo da jumulla 47 a gasar Serie A, ma’ana ya zarta Weah wanda ya zura kwallo 46 lokacin da yake AC Milan.
Dan wasan Napoli a ranar Litinin, a shafinsa na Twitter ya wallafa jindadinsa na kasancewa dan wasan mafi yawan zura kwallo, wanda ya samu damar kamo tarihin Weah.
Sai dai kuma a martanin da ya yi mishi Mai shekara 56 Weah ya taya Dan wasan murnan samun wannan nasara, yana Mai cewa da sannu Osimhen ka iya zama Dan wasa na gaba da zai lashe kyautar Ballon d’Or a nan gaba.