Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciDarajar Lithum: Tattalin arzikin Najeriya zai sami tagomashi | Premier Radio |...

Darajar Lithum: Tattalin arzikin Najeriya zai sami tagomashi | Premier Radio | 13-01-2023

Date:

Karibullahi Abdulhamid Namadobi

 

Yayin da akalar makamashi a fadin duniya ke karkata ga amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki, masana na hasashen nan bada jimawa ba makamashin lithum zai zarta darajar danyen man fetur.

Wannan yasa masu ruwa da tsaki a fannin ma’adanai suka fara jan hankalin gwamnatin Najeriya ta samar da sabbin tsare-tsaren hakowa, hadi da sarrafa ma’adanin lithum din da kasar ke da shi.

Guda daga cikinsu, Engr Haruna Yusuf Beli, Ubandoman rogo ya bayyanawa premier radio cewa matukar aka samar da tsarin da ya dace, sinadarin lithum zai bunkasa hanyoyin samun kudin shigar kasar.

Ya kuma zargi gwamnatin tarayya da yin sakaci a fannin hakar ma’adanai da ka iya ceto kasar nan daga matsalar wutar lantarkin da ta dade tana addabar al’umma.
CUE IN

Ana dai iya samun Lithium a jihohin Kogi, Kwara, Ekiti da cross river a fadin Najeriyar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Shugaba Bola Tinubu ya sauka a kasar China

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a birnin...