Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWacce kwallo kuke tunawa cikin 700 da Ronaldo ya zura a kungiyoyi...

Wacce kwallo kuke tunawa cikin 700 da Ronaldo ya zura a kungiyoyi daban-daban?

Date:

Dan wasan kasar Portugal Cristiano Ronaldo na murnan zura kwallo ta 700 a kungiyoyin da ya fafatawa wasa a duniya.

 

Ronaldo ya zura kwallon ne a wasan da kungiyarsa ta Manchester United ta do ke Everton da ci 2-1 a wasan da suka fafata a filin wasa na Goodison Park a ranar Lahadi.

 

Zakaran kyautar Ballon d’Or har sau Biyar a tarihi, ya samu nasarar zura kwallon da ta bashi damar kafa sabon tarihin bayan da ya shigo sauyin dan wasa Anthony Martial da ya ji rauni.

 

Yanzu haka dan wasa Ronaldo bayan bugawa kungiyoyin kasashen Portugal, England da Spain da kuma Italy ya samu nasarar zura kwallo 700 a tarihin rayuwarsa.

 

Wato a Manchester United zagaye na biyu ya zura kwallo 144 jumulla, Inda kuma ya zura kwallo biyar a Sporting Lisbon..

Sai kuma a tsohowar kungiyarsa ta Real Madrid ya zura kwallo 450, yayin da a Juventus kuwa ya zura kwallo 101.

 

Ronaldo a wadannan kwallayen dai akwai da dama magoya bayansa suke tunasu, musamman yadda su kai tasiiri a nasarar da kungiyoyin da ya wakilta su kai a baya.

 

A gefe guda kuwa kwallo biyun da Ronaldo ya zura a ragar Jamhuriyar Ireland ya sa ya hada 111 jumulla daga matakin kasa, wanda hakan ya sanya ya haura Ali Daei mai kwallo 109 a raga a tawagar Iran tsakanin 1993 zuwa 2006.

 

Haka kuma Ronaldo shi ne na gaba a cin kwallaye a Champions League da 140, wato ya bai wa Lionel Messi abokin hamayyarsa tazarar 13.

 

Sai kuma Ronaldo yana gaban Messi a yawan cin kwallaye a kungiyoyin da yake buga wa wasanni, bayan da kyaftin din Argentina keda 691 a fafatawar da ya yi Barcelona da Paris St Germain.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Sabbin Yan Wasa 12 da Kano Pillars ta dauka

Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars, wadda ta lashe...