Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKaso 60 na dalibai ne suka ci jarrabawa a bana-NECO

Kaso 60 na dalibai ne suka ci jarrabawa a bana-NECO

Date:

Dalibai sama da 700,000 ne suka ci jarrabawar kammala sakandire ta 2022 wadda Hukumar Tsara Jarrabawa ta Kasa NECO ke shiryawa.

Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai a Minna.

Ya ce masu ruwa da tsaki da dama sun tantance cewa an samu gagarumar nasara a jarrabawar kammala sakandire da hukumar ta yi a shekarun baya-bayan nan.

Wushishi ya ce a cikin dalibi 1,198,412 da suka rubuta jarrabawar, dalibi 727,864 wato kashi 60.74 ne suka ci jarrabawar da fiye da darasi biyar ciki har da Ingilishi da Lissafi.

Farfesa Ibrahim Wushishi ya shawarci daliban da suka rubuta jarrabawar su duba shafin hukumar NECO don ganin sakamako

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...