Sanata Ndume ya dora alhakin tabarbarewar kasarnan a wuya masu bawa Tinubu shawara.

0
95

Sanata Ndume ya dora alhakin tabarbarewar kasarnan a wuya masu bawa Tinubu shawara

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawan kasar nan, kuma tsohon bulaliyar majalisar Sanata Ali Ndume ya sake kalubalantar gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, tare da dora alhakin tabarbarewar al’amura a kasar nan kan masu bashi shawara da ya nada.

Sanata Ndume cikin wani sako da ya fitar ga manema labarai a karshen makon nan, ya zargi masu baiwa shugaban kasar shawarar da kin fada masa gaskiya.

A cewar Ndume daukacin masu baiwa shugaban kasar shawara su ne suka dauki kaso mai tsoka a hannu wajen hargitsa wannan kasa, kuma a fahimtarsa basa nufin wannan kasa da alkhaiiri.

Ya kara da cewa shi akankin kansa ya gamsu cewa manufofin shugaban kasa Tinubu manufofi ne masu tasiri wajen bunkasa rayuwar yan kasar nan, amma wasu daga cikin masu baiwa shugaban kasar shawara ne kan gurgunta manufofi ta yadda a karshe maimakon talaka ya samu sa’ida sai ya koma cikin yanayi na kaka-ni-kayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!