Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBa zamu hana Kwankwaso da Atiku siyan form ba-PDP

Ba zamu hana Kwankwaso da Atiku siyan form ba-PDP

Date:

Jam’iyar PDP ta ce ba za ta Hana Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Kwankwaso siyan Takardar yin yin takarar a cikin ta ba.

A cewar jam’iyyar har yanzu ba ta tsaida matsaya a kan ko wanne ɓangare ne na ƙasar nan zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba.

Ta ce ta yanke shawar fara sayar da fom ɗin takara ne domin kada ta saɓa wa wa’adin da Hukumar Zaɓe ta INEC ta sanya.

Shugabancin jam’iyar ya ce sabo da jadawalin da INEC ta fitar, shi ya sanya ba a hana kowa ya sayi fom ba, musamman ma Atiku Abubakar da Rabi’u Kwankwaso.

Tuni dai Atiku Abubakar ya sayi fom ɗin takararsa, akan kudi Naira miliyan 400, inda ya ce wata kungiyar ƴan kasuwa a Arewa ce ta sai masa.

Bayan Atiku da Kwankwaso, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ma na neman takarar shugabancin kasar a jam’iyar adawa ta PDP.

Hakazalika gwamnonin PDP na shiyyar kudu sun bi sahun ƴanuwan su na APC wajen tsaya wa a kan cewa dole ɗan takarar shugabancin kasa daga ɓangaren su zai fito.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...