Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWawa ne kadai zai iya sasanci da yan ta'adda-Masari

Wawa ne kadai zai iya sasanci da yan ta’adda-Masari

Date:

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce a yanzu marar hankali ne kawai zai iya yin sulhu da ‘yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilan majalisar Dinkin duniya a fadarsa ranar Asabar.

Ya ce a baya gwamnatinsa ta shiga sulhu da yan bindigar, Amma suka Saba duk ka’idoji da sharuddan da aka cimma.
“Ba zan kara gasgata Yan bindiga ba, yan ta’adda ne, barayi ne da Basu da wani tunani.

“Abinda suka sanya a gaba shi ne kashe jama’a kawai, suna fakewa da addini” Ya ce.

Gwamnan ya kuma tabo batun yadda rashin tsaro ya faro a kasar nan tun daga shekarar 1903.

Ya kuma bukaci majalisar Dinkin duniyar ta yi amfani da damar da take da shi wajen Hana shigowa da yaduwar Malamai a kasar nan.

Ya kuma ce akwai bukatar tallafawa Arewacin kasar nan da kayan tsaro na zamani da zai taimaka wajen shawo kan matsalar cikin sauki.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories