Kungiyar ƙwallon kwando ta Kano Pillars ta kai wasan Super 8 a gasar ƙwallon kwando ta ƙasa (NBBF Premier League) bayan doke Aso Sky Hawks ta Abuja da ci 84-81 a Minna da ke jihar Neja.
Tawagar da ake wa lakabi da Pyramids City Boys ta samu nasara a wasanni biyar a wannan mataki, inda ta doke Niger Potters, Gombe Bulls, Bauchi Nets, City Chiefs ta Jihar Benuwai da kuma Aso Sky Hawks.
Sai dai ta yi rashin nasara a wasa guda ne kawai a hannun Nile University ta Abuja.
Wannan nasarar ta tabbatar wa Kano Pillars damar shiga cikin manyan ƙungiyoyi huɗu daga kowanne bangare na gasar wato Savannah da Atlantic Conferences, domin fafatawa don lashe kofin gasar tare da neman tikitin shiga gasar neman cancantar FIBA Zone 3 da za a gudanar daga baya a wannan shekara.
Sakataren kungiyar Kano Pillars Basketball Club, Bashir Musa, ya bayyana nasarar a matsayin jajircewa ga sabbin shugabancin hukumar Wasanni ta Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Tukur Babangida.
Ya ce duk da matsalolin kuɗi da ƙungiyar ke fuskanta, ‘yan wasan sun ci gaba da nuna jajircewa da mayar da hankali wajen ganin sun ci gaba da samun kyakkyawan sakamako a gasar.
Bashir Musa ya kuma ya bawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bai wa ƙungiyar, tare da kira ga ‘yan wasan da su ci gaba da ƙoƙari domin cimma manufofin kungiyar.
A halin yanzu ana gudanar da zagaye na biyu na gasar NBBF Premier League a lokaci guda a cibiyoyin Minna da Enugu.
